An samu mutuwar aƙalla mutum 5, an kuma kuɓutar da mutum 30 bayan wani haɗarin jirgin ruwa a jihar Anambra da ke Najeriya.
Jirgin ya kife ranar Lahadi a hanyar kogin Niger da ke Kudu maso Yammacin jihar ta Anambra.
Mai magana da yawun rundunar ƴan sanda a jihar, Tochukwu Ikenga ya shaida wa kafafen yaɗa labarai cewa mahukunta suna kan gudanar da bincike domin gano dalilin afkuwar haɗarin .
Kifewar jiragen ruwa na yawan faruwa a Najeriya dalilin rashin kulawa da kuma rashin mutunta dokokin kare kai ciki har da cika jiragen da mutane da kayayyakin da suka wuce ƙima.