Akalla mutane biyar ne suka mutu sannan wasu 60 kuma suna kwanta a asibiti, sakamakon barkewar cutar kwalara a kewayen yankin Eti Osa da Island da Ikorodu da Kosofe na jihar Legas.
Kwamishinan lafiya na jihar Legas, Akin Abayomi, ne ya bayyana hakan yayin da yake mayar da martani game da barkewar cutar.
Abayomi ya ce gwamnatin jihar ta fitar da wani kira na a kara sanya ido tare da daukar matakan kariya, domin dakile bazuwar cutar kwalara a jihar.
Ya kara da cewa, abin bakin ciki, an samu rahoton mutuwar mutane biyar musamman daga majinyatan da suka makara tare da matsanancin rashin ruwa a jikin su.
Kwamishinan ya kara da cewa, biyo bayan ruwan sama da aka yi a baya-bayan nan, jihar Legas ta samu karuwar masu fama da matsananciyar amai da gudawa, inda y ace, matsugunan birane da cunkoson jama’a da rashin tsaftar muhalli na cikin hadari.