Akalla mata 46 ne aka kashe a wata tarzoma a gidan yarin mata da ke Honduras.
Hukumomin kasar na ci gaba da ƙokarin zaƙulo gawarwakin fursunonin, wadanda da yawansu suka kone kurmus a lokacin da wasu abokan gabar su suka haddasa gobara, wasu an harbe su ne, kuma wasu caka musu wuka aka yi
Ana ci gaba da bincike domin gano yadda fursunonin suka yi nasarar shigo da makamai masu sarrafa kansu da adduna zuwa cikin gidan yari.
Shugabar kasar Honduras, Xiomara Castro, ta ce an shirya tarzomar da sanin jami’an tsaron gidan yarin.
Ta shirya daukar tsauraran matakai don magance tashe-tashen hankula a nan gaba.
Dama an sha fama da rikicin gidan yari irin wannan a Hondurus.


