Hukumar Kiyaye Aukuwar Hadura ta Kasa ta ce, mutum 412 ne suka mutu yayin da mutum 522 suka samu munanan raunuka a haÉ—uran ababen hawa da suka auku a hanyoyin Legas tsakanin watan Janairu zuwa Oktoba.
Babban jami’in hukumar mai lura da shiyyar Legas Olusegun Ogungbemide -wanda ya wakilci babban shugaban hukumar – a taron ranar tunawa da waÉ—anda hatsarin kan tituna ya rutsa da su ne ya bayyana haka a birnin na Legas.
Ya ƙara da cewa bincike ya nuna cewa gudun wuce kima, da rashin gyaran ababen hawa, da tuƙin ganganci a matsayin abubuwan da suke haddasa aukuwar mafi yawan haduran da ake gamuwa da su.
Ya ci gaba da cewa sauya wa direbobi É—abi’a game da waÉ—ancan abubuwa da na da matuÆ™ar muhimmanci, wajen rage aukuwar hasuran.