Bayanai daga jihar Kaduna sun ce aƙalla mutum 40 ne masu Mauludi suka rasu da yammacin ranar Lahadi, sakamakon wani haɗari inda wata babbar motar kaya ta hau kan wata mota ƙirar JF ɗauke da mutum fiye da 70.
Wani wanda ɗaya ne daga masu shirya Mauludin ya shaida wa BBC cewa “daga garin Kwandari za su zo nan Saminaka a daidai Lere kan kwana wata babbar mota ta hau kan motarsu. An ce wani mai babur ne ya gifta wa direban babbar motar inda shi kuma mai babbar motar ya kauce masa abin da ya sa ya hau kan motar masu Mauludin.”
Bayanan sun ce aƙalla mutum 30 ne suke a asibiti inda suke samun kulawa.
Wani wanda shi ne mutumin da ya ɗauki alƙaluma bayan haɗarin ya ce “waɗanda suka mutu su 41 ne mata guda 19 da ƙananan yara 10 da sauran mutane musamman tsaffi kusan 11 sai kuma masu rauni fiye da 30.”