fidelitybank

Mutane 39 sun kamu da cutar kyandar Biri a Najeriya – Ministan Lafiya

Date:

Gwamnatin tarayya, ta ce, ta tsaurara matakan bincike a dukkan hanyoyin shigarta domin daƙile yiwuwar shiga da cutar ƙyandar Biri cikin ƙasar nan.

Wannan na zuwa ne bayan hukumar hana yaɗuwar cutuka ta Afirka, da ma Majalisar Dinkin Duniya sun ƙaddamar da dokar ta ɓaci a kan yaƙi da cutar ta ƙyandar Biri da ake kira da Mnkey pox.

Da yake sanar da matakan da hukumomi a a kasar nan ke ɗauka domin kare jama’a daga wannan cuta, ministan lafiya Farfesa Muhammad Pate, ya ce, za a tsaurara bincike a kan masu shiga Najeriya daga kowanne ɓangare, domin tabbatar da ganin wani daga waje bai shigar da ƙwayar cutar cikin ƙasar ba.

Sanarwar da Ministan ya fitar ta ce cibiyar daƙile yaɗuwar cutuka ta ƙasar ta sanar da gwamnati da cewa an samu mutum 39 da suka kamu da cutar ƙyandar Biri a Najeriya.

Ministan ya ce daga alƙalumman da hukumomi suka tattara daga farkon wannan shekarar, an samu masu cutar ne a jihohi 33 da birnin tarayya Abuja, kuma kawo yanzu babu wanda ya mutu sanadiyyar cutar.

Saboda haka ne ministan ya ce gwamnati ta yi saurin samar da tsarin yin gwaji ga duk wanda zai shiga Najeriya, domin gano cutar tun kafin a shigar masu da annoba.

Itama hukumar hana yaduwar cutuka ta Najeriyar ta jaddada wannan matakin da gwamnatin tarayyar ta sanar, kuma shugaban ta Dr Jide Idris, ya yi bayanin cewa sun ƙara matakan yin gwaji a filayen jiragen saman ƙasa da ƙasa guda 5 da ake da su a ƙasar, da tashoshin ruwa 10 da kuma iyakokin kan ƙasa guda 51, duk dai a ƙoƙarin hana shiga da cutar.

Hukumomi a Najeriyar dai sun kuma sanar da tsaurara matakan tantance masu ɗauke da cutar a jihohin Legas da Enugu da Rivers da Cross Rver da Akwa Ibom da kuma Adamawa.

Sauran jihohin sun haɗa da Taraba da Kano da kuma birnin tarayya Abuja.

punch newspaper

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp