fidelitybank

Mutane 37 a ka yanke wa hukunci a Kano – NDLEA

Date:

Kimanin masu safarar miyagun kwayoyi 37 da masu amfani da muggan kwayoyi ne hukumar yaki da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa reshen jihar Kano ta yankewa hukunci tsakanin watan Janairu zuwa Maris.

Mista Abubakar Idris-Ahmad, Kwamandan Hukumar na Jihar, ya bayyana a ranar Litinin cewa, rundunar ta kama mutane 352 da ake zargi a cikin wa’adin.

Ya bayyana cewa rundunar ta shigar da sabbin kararraki 39, yayin da wasu 127 ke kan kararraki, baya ga 37 da babbar kotun tarayya ta yankewa hukunci.

Karanta Wannan: Za mu hukunta masu yaÉ—awa muna neman ma’aikata – EFCC

Ya ce, “Tsakanin watan Janairu zuwa Maris, an kwace 955.304kg na cannabis sativa, 1,225.05kg na Codeine da Tramadol, gram 25 na hodar iblis, giram 17 na heroin da gram 52 na methamphetamine.”

Ya kuma bayyana cewa rundunar ta samu ci gaba mai kyau a kokarinsu na rage bukatun muggan kwayoyi inda aka wayar da kan mutane 5,060 da suka hada da daliban sakandare da manyan makarantu, kungiyoyin ‘yan kasuwa, kungiyoyin ’yan banga da ‘yan bangar siyasa da dai sauransu, kan illar shaye-shayen miyagun kwayoyi.

Ya kuma yi kira ga mazauna garin da su rika fadakar da hukumar a ko da yaushe da bayanan ayyukan dillalan miyagun kwayoyi a cikin al’ummarsu da nufin dakile ayyukansu.

Ya ba da tabbacin cewa za a iya cimma hakan ne yayin da sauran jama’a da iyaye da kuma shugabannin al’umma suka zama masu sa ido a unguwanninsu don magance matsalar fataucin miyagun kwayoyi da shaye-shayen miyagun kwayoyi.

Ya kuma tabbatar da cewa hukumar ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi a jihar da sauran sassan kasar nan.

Ya bayyana cewa rundunar za ta ci gaba da zagayawa a kowane lungu da sako na jihar domin tabbatar da an samu al’ummar da ba ta da muggan kwayoyi.

nnn hausa

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp