Mataimakin shugaban kasa, Kassim Shettima, ya ce yawan mutanen da suka mutu sakamakon hare-haren ƙunar baƙin wake da aka kai garin Gwoza a jihar Borno ya ƙaru zuwa 32.
Shekttima ya sanar da haka ne lokacin da ya kai ziyarar ta’aziyya zuwa jihar ta Borno game da ibtila’in da ya faru. Ya ƙara da cewa cikin mutum 42 da aka kai asibiti bayan harin, an sallami mutum 14.
A cewarsa, har yanzu mutum 26 na samun kulawar likitoci.
Mataimakin shugaban ƙasar ya kuma bai wa dukkanin mutanen da ibtila’in ya rutsa da su tallafin kuɗi tare da yi wa iyalan waɗanda suka mutu jaje.
“Zuwa yanzu an samu mutum 32 da suka mutu, an kawo mutum 42 daga Gwoza kuma an sallami kimanin mutum 14 amma mutum 26 har yanzu suna jinya a asibiti.
“Ina amfani da wannan dama na miƙa godiya ga gwamnatin jihar Borno da hukumar bayar da agajin gaggawa ta ƙasa da ta jiha da kuma ƙungiyar ICRC saboda gudummawar da suka bayar,” in ji shi.