Aƙalla mutum talatin ne suka mutu aka kuma kwantar da gommai a asibiti bayan da suka sha wata giya haɗin gida a gundumar Kallakuruchi da ke jihar Tamil Nadu da ke kudancin Indiya.
Hukumomi sun ce yawancin waɗanda aka kwantar a asibitin sama da 80 suna fama ne da amai da gudawa da kuma ciwon ciki bayan sun sha giyar ta burkutu a ranar Talata da daddare.
An kama jami’ai goma da suka haɗa da wani babban jami’in haraji da Baturen ƴansanda a kan lamarin.
Babban minista na jihar ta Tamil Nadu, MK Stalin ya rubuta a shafinsa na sada zumunta da muhawara cewa lamarin ya girgiza shi.
Ministan ya kuma sanar da diyyar dala dubu 12 ga iyalan waɗanda suka mutu, su kuwa waɗanda aka kwantar a asibiti za a ba kowane mutum ɗaya dala 600.
KOwace shekara gomman mutane suna mutuwa a Indiya sakamakon shan giyar da ake yi ta gargajiya, inda yawanci ake sanya mata sinadarai da suka wuce kima.