fidelitybank

Mutane 3 sun mutu a wani mumunan hadarin mota a Yobe

Date:

Mutane uku ne suka mutu a wani mummunan hatsarin mota da ya rutsa da wata mota kirar saloon da wata motar bas mai mutane 18 a kan babbar hanyar Jakusko zuwa Gashuwa a jihar Yobe da sanyin safiyar Lahadi.

Motocin da suka yi taho mu gama daga bangarori saboda tsananin gudu kuma nan take suka tashi da wuta, kamar yadda wani ganau ya shaida.

Marigayin wadanda suka hada da: Malam Usman Bahago Arfani, Adamu Umar Sanda da Abba Saleh Abba Kyari Gashua, an ce suna cikin motar saloon kuma dukkansu ’yan asalin garin Gashu’a ne.

An kuma tattaro cewa fasinjoji da dama daga cikin motar bas ta kasuwanci sun samu raunuka musamman sakamakon gobara da aka kai su babban asibitin Jakusko domin kula da lafiyarsu.

Hakan dai ya zo ne sa’o’i 24 bayan hukumar kiyaye hadurra ta tarayya a cikin sakon watan Ramadan, ta yi kira ga ‘yan Najeriya da su yi cikakken biyayya ga dukkan ka’idojin zirga-zirgar ababen hawa da gwamnati ta kafa domin kula da tsaftar hanyoyin.

nigeria peace corps

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp