Mutum uku ne suka mutu cikin kwana guda sakamakon raunukan da suka ji a bikin hawan kaho da aka gudanar a gabashin kasar Sifaniya.
Lamarin ya faru ne a yankin Valencia, inda aka gudanar da bukukuwan hawan kahon, lokacin da wasu manyan bijimai suka kwato tare da nufowa cikin gari, yayin da mutane suka rika gudu don tseratar da rayukansu.
kungiyoyin kare hakkin dabbobi dai sun sha yin korafe-korafe, game da hatsarin da ke tattare da wannan wasa ga mutane da ma su kansu dabbobin.
Suna masu cewa mutum 20 ne suka mutu a yankin cikin shekara takwas sakamakon wannan wasa.
Duka mutane ukun da suka mutu, sun samu munanan raunuka ne lokacin da lamarin ya faru makonni biyu da suka gabata. In ji BBC.
Daya daga cikinsu ya gamu da ajalinsa ne lokacin da wani bijimi ya yi awon-gaba da shi yayin da ya same shi tseye a gefen wani gini.
Sannan akwai wani mai shekarar 50 da wani katon bijimi ya soka masa kaho a cikinsa, a garin Meliana da ke arewacin Valencia
Sai kuma wani Bafaranshe mai yawon bude-ido da shi ma ya mutu a ranar Litinin sakamakon raunin da bijimin ya ji masa lokacin da ya kwada shi kan wani katon dutse.