Yan sanda a Ukraine sun ce wani kansilan ƙauye a yammacin ƙasar ya jefa gurneti a cikin ɗakin da majalisar ƙaramar hukumar ke zama, tare da raunata mutum 26.
Lamarin ya faru ne da safiyar ranar Juma’a, a shelkwatar ƙaramar hukumar Keretsky ta jihar Transcarpathian da ke yammacin ƙasar.
Kawo yanzu ‘yan sanda ba su ce komai ba kan manufar harin, wanda mutum shida suka samu munanan raunuka.
A lokacin da abin ya faru ana tsaka da haska zaman majalisar kai-tsaye a shafin Facebook
Kansilolin na tsaka da zazzafar muhawara kan kasafin kuɗin ƙaramar hukumar na shekarar 2024, tare da kuɗin da ƙaramar hukuma ta kashe a wannan shekara da kuɗaɗen garaɓasar da shugaban kansilolin zai samu.
Kimanin sa’a ɗaya da rabi kafin fara zaman, an hasko ɗaya daga cikin kansilolin na magana da ƙarfi, inda yake nuna adawa da kasafin kuɗin, daga nan sai ya fice daga zauren, tare da wani mutum.