fidelitybank

Mutane 26,800 ke mutuwa duk shekara sanadiyar taba Sigari a Najeriya

Date:

Gwamnatin Najeriya ta ce mutane 26,800 ke mutuwa a duk shekara, a sanadiyyar cututtukan da suka shafi sinadarin Tobacco, yayin da ƴan ƙasar miliyan 4.5 daga shekara 15 zuwa sama ne ke tu’ammali da sinadarin.

Hakan na ƙunshe ne a wata sanarwar da hukumar kare masu amfani da kayayyaki ta ƙasar ta fitar a ranar Litinin.

Muƙaddashin hukumar, Adamu Abdullahi, ya bayyana hakan ne a wajen ƙaddamar da wani shirin daƙile amfani da sinadarin na Tobacco wanda ke ƙunshe a taba sigari da wasu abubuwa.

Shirin da aka sanya wa suna ‘kada ka ƙona makomarka’.

Adamu ya ce shirin na fatan magance ƙaruwar da ake samu na amfani da kayayyakin da ke ɗauke da sinadarin a tsakanin masu tasowa da kuma masu ƙarancin shekaru.

Inda ya ƙara da cewa shirin na kuma neman magance matsalolin da hakan ke janyo wa ga al’umma baki ɗaya.

Shugaban ya kuma jaddada muhimmancin samun ƙoshin lafiya, wanda ta haɗa da lafiyar gangar jiki da ta ƙwaƙwalwa da ta kuma walwala.

Adamu ya kuma nuna muhimmancin haɗa ƙarfi waje guda domin samar da manyan gobe masu ƙoshin lafiya.

Ya bayyana wasu daga cikin illolin tu’ammali da sinadarin tobacco ga matasa da suka haɗa da illa kan ƙwaƙalwa da hanyoyin numfashi da kuma yadda rayuwa ke ta’allaka da sinadarin nicotine.

daily post

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp