Daga birnin Edinburgh, gwamnatin kasar Scotland ta wallafa wani sakon Tiwita da ke cewa layukan mutanen da ke son ganin gawar Sarauniya a cocin St Giles sun kare.
Gwamantin ta ce fiye da mutum 26,000 ne suka sami damar karrama Sarauniyar, ciki har da wadanda suka kwana suka jiran a ba su damar shiga cocin.
Wasunsu sun ce an shaida mu su cewa za su rasa damar kafin a dauke ta daga cocin zuwa birnin Landan. In ji BBC.