A ranar Laraba ƙungiyar agaji ta ƙasa da ƙasa Red Cross a Najeriya ta ce, ƙasar ta samu mutum sama da 25,000 da suka ɓata cikin shekaru 10 da suka gabata.
Da yake zantawa da manema labarai, jami’in hulɗa da jama’a na ICRC a Najeriya Aliyu Dawobe, ya bayyana an samu adadin ne bayan da ƴan uwan mutane suka zo suka shigar da batun a wurin ƙungiyar ta Red Cross.
Dawobe ya ce, “ICRC ta fara haɗa kan iyalai ne a shekarar 2013 a Najeriya.
Ya ce mutum 25,000 da suka ɓace kaɗan ne daga cikin mutanen da suka san cewa ICRC na taimakawa wajen haɗa ’yan uwa da suka rabu da iyalansu.
Dawobe ya ce sun yin rajistar korafe-korafensu kuma akwai fiye da batutuwa 25,000 da aka shigar gaban ICRC.
Sai dai jami’in na ICRC ya ce alkaluman mutanen da suka ɓata a Najeriya a cikin shekaru goma da suka wuce za su iya raguwa sakamakon cewa wasu iyalai na sake haɗuwa da ƴan uwansu ba tare da taimakon ƙungiyar Red Cross.