Adadin mutanen da aka tabbatar sun mutu sakamakon girgizar kasar da aka yi a Turkiyya da Syria ya ƙaru zuwa sama da 24,000
Miliyoyin mutane sun rasa gidajensu a yankunan kuma masu aikin ceto suna ƙara mayar da hankali kan wadanda ke bukatar abinci da muhalli.
Majalisar Dinkin Duniya ta ce kusan mutum dubu dari tara ne ke buƙatar abinci cikin gaggawa a sassan Turkiyya da Syria.
Babban jami’in jin kai na Majalisar Ɗinkin Duniyar ya ce zuwa yanzu tawagar agaji biyu ce kaɗai ta isa yankunan da ‘yan tawaye ke riƙe da su a Syria.