Gwamnan jihar Ondo, Arakunrin Oluwarotimi Akeredolu, ya bayyana cewa mutane 80 harin ta’addancin da aka kai ranar Lahadin da ta gabata a cocin St Francis Catholic da ke titin Owa-luwa, Owo ya shafa.
Gwamna Akeredolu ya ce, mutane 22 ne suka rasa rayukansu sakamakon wannan mummunan harin, yayin da wasu 52 da suka tsira da rayukansu ke kwance a cibiyar lafiya ta tarayya, Owo, Asibitin St Louis, Owo da babban asibitin Owo da kuma wasu asibitoci masu zaman kansu.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a ranar Talata a yayin wani jawabi ga al’ummar jihar kan harin ta’addancin da aka kai a ranar Lahadin da ta gabata a cocin St. Francis Catholic Church, dake titin Owaluwa, Owo.