fidelitybank

Mutane 209 ne suka mutu sakamakon fashewar Tankar fetur – Kwamiti

Date:

Kwamitin binciken fashewar tankar mai na jihar Jigawa ya ce, mutane 209 ne suka rasu, sannan mutum 99 suka jikkata, bayan kadarorin miliyoyin naira da aka rasa a ibtila’in wanda ya auku a ranar 14 ga Oktoba a garin Majiya da ke jihar ta Jigawa.

Kwamitin, wanda Hafizu Inuwa ya jagoranta ne ya bayyana hakan a lokacin da yake miƙa rahoton bincikensa ga gwamna Umar Namadi a ranar Laraba kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Rahoton kwamitin ya kuma nuna cewa har yanzu akwai mutum 38 da suke jinya a asibiti a sanadiyar lamarin wanda ya shafi iyalai 167.

Kwamitin ya kuma bayar da shawarar a riƙa kiyaye wajen sufurin man fetur, sannan ya buƙaci a samar da sashen kula da tashin hankali a asibitoci, sannan a kafa hukumar kula sufuri domin tabbatar da bin dokar tuƙi.

A nasa ɓangaren, gwamnan jihar ya yaba wa mambobin kwamitin bisa aikin da suka yi, sannan ya ce a shirye suke su aiwatar da shawarwarin da kwamitin ya bayar.

latest legit news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp