Akalla mutane ashirin ne suka mutu sakamakon wani rikicin kabilanci da ya barke tsakanin kabilun Wurkunawa da kuma Karimjo a Karamar Hukumar Karim Lamido ta jihar Taraba.
An kuma kona gidaje da dama da asarar dukiya mai dimbin yawa.
Tashin hankalin ya samo asali ne kan batun sarautar gargajiya a yankin.
A cikin makon da ya gabata ne gwamnan jihar ta Taraba Darius Ishaku ya bai wa Alhaji Yakubu Abubakar Haruna sanda a matsayin sabon sarki a masarautar Wurkum da ke Karamar Hukumar Karim Lamido a jihar Taraba.
An nada sarkin ne bayan rasuwar mahaifinsa da ya shafe shekara 47 yana mulki.
BBC ta tattauna da dukkan bangarorin da ke rikici da junan kuma shugaban kungiyar ci-gaban al’ummar Wurkum na duniya Wilfred Habuba Yambakam Kwanchi, ya ce dukkan bangarori sun yi asara a rikicin.
“An dan samu zaman lafiya a cikin gari amma a kauyuka inda Wurkunawa suke har yanzu ana ta’adi, ana kona gidajen mutane sannan an kashe wasu yara.
Abincin gidaje da dabbobinsu ma duk an tafi da su, an yi asarar rayuka kuma a halin yanzu ba za mu iya cewa ga adadin mutanen ba amma sun fi goma sha biyar” a cewar Wilfred.
Ya kara da cewa gwamnati ta tura jami’an tsaro a yankin da lamarin ya auku.
Sannan yayi zargin cewa tun ranar da aka nada sabon sarki na garin wanda dan kabilar Wurkunawa ne sai ‘yan kabilar Karimjo suka fara kone-konen tayoyi a cikin garin Karim Lamido.
Wilfred Habuba ya ce dama masarautar ta Wurkunawa ce sannan babu batun takara kan masarautar daga dukkan kabilu da ke yankin.