Sama da ‘yan kungiyar Boko Haram da na Islamic State of West Africa (ISWAP) 20 ne a ka tabbatar da cewa an kashe su a wani samamen da sojojin hadin gwiwa na sama da na kasa da su ka yi na tsawon mako guda da sojojin Najeriya da na Nijar a tafkin Chadi.
A cewar wata sanarwa a ranar Juma’a, 24 ga watan Disamba ta hannun rundunar hadin gwiwa ta Multinational Joint Task Force (MNJTF) reshen 4 mai shelkwata a yankin Diffa da ke Kudu maso Gabashin Nijar, an kashe sojoji shida daga Najeriya da Nijar yayin farmakin da jiragen yaki da kuma abokan Amurka ke marawa baya.
Shirin na MNJTF na tsawon mako uku mai suna Sharan Fage, wanda a ka gudanar da shi ne a matakai biyu a yankin tafkin Chadi na Najeriya tsakanin 1 zuwa 21 ga watan Disamba.
Akalla mahara 22 ne su ka mutu a harin yayin da sojojin Nijar da na Najeriya 23 suka samu raunuka tare da lalata motoci biyu.
Sanarwar ta kara da cewa sojojin na hadin gwiwa sun fuskanci hare-hare daga da harin gaba da wata mota kirar bama-bamai (VBIED) ta kai.
A ranar 14 ga watan Disamba, kungiyar ISWAP ta yi ikirarin kai harin kunar bakin wake da a ka kai da mota a kan sojojin Najeriya da na Nijar kwanaki kadan da suka gabata.
An gudanar da aikin kashi na farko a garin Malam Fatori kusa da gabar tafkin Chadi. Ya hada da katangar garin, domin tallafawa kokarin sake tsugunar da su.
Kashi na biyu ya shafi ayyuka a Arege, Gashigar, Asaga, da Kamagunma.
Har ila yau, aikin ya yi sanadin kwatowa tare da lalata motoci, da babura da kuma makaman atilare da ke nuni zuwa birnin Diffa.