fidelitybank

Mutane 20 sun mutu bayan sun kwankwadi Barasa

Date:

Mutane kusan 20 suka mutu a Morocco, bayan sun sha wata barasa mai guba a wani kantin gefen titi da ke birnin Ksar el-Kebir na arewacin kasar.

An kuma kai wasu gommai zuwa asibiti cikin mawuyacin hali, inda mutum biyu ke kwance a dakin kula da masu matsananciyar jinya.

Hukumomi sun kama wani mutum mai shekara 48 bisa zargin hannu a lamarin. Yayin da ‘yan sanda suka ce sun gano kimanin lita 50 ta ruwan barasar a shagonsa.

Haramun ne sayar da barasa a kasar Moroko, sai dai rahotanni sun ce sau da yawa ana sayar da gidajen cin abinci da kantuna a fakaice. In ji BBC.

A watan Agusta, mutum takwas ne aka ba da rahoton mutuwarsu bayan sun sha gurbatacciyar barasa a yankin Oriental na arewacin kasar.

Kimanin mutum 20 kuma sun mutu a watan Yulin bara a irin wannan lamari da ya faru a Oujda, da ke gabashin Moroko.

naija news today

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp