fidelitybank

Mutane 18 sun tsallake rijiya da baya a wani hadarin mota

Date:

Wasu mutane sha takwas sun tsallake rijiya da baya, a ranar Alhamis yayin da wata mota kirar Toyota Hiace mai kujeru 18 ta kama wuta a kan hanyar ta.

Lamarin da ya afku a kauyen Koko Araromi, daura da titin Ajase Ipo, a jihar Kwara, ya sa masu ababen hawa da dama suka makale.

Motar da aka ce ta na kan hanyar zuwa Osdogbo a jihar Osun ta kama wuta da misalin karfe 10:57 na safe a kan hanyar.

Duk da cewa ba a samu asarar rai ba yayin da fasinjojin suka yi gaggawar sauka daga motar bas din, duk da haka kayayyakinsu da jakunansu sun kone kurmus.

Kwamandan hukumar kiyaye hadurra ta kasa (FRSC) a jihar Jonathan Owoade, ya tabbatar wa Aminiya faruwar lamarin a wata tattaunawa ta wayar tarho.

Owoade wanda ya danganta lamarin da kwararar mai daga motar ya ce, “Hukumar kula da kiyaye hadura ta kasa ta dakatar da motocin da ke zuwa na wasu mintuna saboda tsananin gobarar.”

vanguard news today

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Zulum ya miƙa kyautar Naira miliyan 100 ga iyalan Sojojin da aka kashe

Gwamna Babagana Umara Zulum na jihar Borno, ya bai...

Otal ɗin ƴan Najeriya ya kama da wuta wani ɓangaren a Saudiyya

Hukumar Alhazai ta Najeriya ta ce an samu tashin...

An kai hari maɓoyar Boko Haram a Borno

Biyo bayan sahihan bayanan sirri da aka samu, rundunar...

Alaƙar Trump da Elon Musk ta yi tsami sosai

Attajirin da ya fi kowa arziki a duniya, Elon...

An yi jana’izar Muhammad Uwais

An gudanar da jana'izar tsohon alkalin alkalan Najeriya, mai...

Musulman Nijeriya a cigaba da jajircewa – Obi

Ɗan takarar shugaban ƙasa a karkarshin jam'iyyar Labour a...

Akwai takaici ambaliyar Neja – IBB

Tsohon shugaban ƙasa, Janar Ibrahim Babangida, ya kwatanta ambaliyar...

Farfesa Jibril Aminu ya rasu ya na da shekaru 86

Allah ya yi wa Farfesa Jibril Aminu mai shekara...

Alhajin Najeriya ya rasu a tsayuwar Arfa

Wani Alhaji daga Najeriya ya rasu a filin Arfa...

Alhazai miliyan 1.673,230 ne ke gudanar da akin Hajji – GASTAT

Hukumar tattara alƙaluma ta Saudiyya (GASTAT) ta ce, Alhazai...

Isra’ila ta gano gawar ƴan ƙasarta

Rundunar sojin Isra'ila ta ce ta gano gawar ''yan...

Ma’aikatan wutar lantarki a Abuja sun fusata

Ma'aikatar kamfanin rarraba wutar lantarki na Abuja Electricity Distribution...
X whatsapp