Akalla mutum guda ya rasu a yayin da aka ceto wadansu 18 sakamakon hatsarin kwale-kwale da ya faru a kauyen Kwalgwai da ke karamar hukumar Auyo a jihar Jigawan Najeriya.
Lamarin ya auku ne a ranar Lahadi da daddare kuma har yanzu ba a ga mutum daya ba daga cikin wadanda ke cikin kwale-kwalen.
Wata sanarwa da kakakin ‘yan sanda a jihar ta Jigawa, DSP Lawan Shiisu Adam ya fitar, ta ce wadanda ke cikin kwale-kwalen maza ne da mata.
Binciken da ‘yansanda suka gudanar ya nuna cewa hatsarin ya auku ne sakamakon daukar mutane fiye da kima a cikin kwale-kwalen.


 

 
 