fidelitybank

Mutane 18 sun mutu a titin Bauchi

Date:

Mutum aƙalla 18 ne suka ƙone ƙurmus sakamakon wani hatsarin mota da ya afku a Ƙaramar Hukumar Toro ta Jihar Bauchi, inda motar bas ta yi taho-mu-gama da tirela ranar Laraba.

Kwamandan yanki na hukumar kiyaye haɗurra ta ƙasa, Yusuf Abdullahi, ya ce hatsarin ya faru ne a ƙauyen Narbodo, kamar yadda kamfanin labarai na NAN ya ruwaito cewa. Kwamandan ya ce, hatsarin ya ƙunshi motar bas ƙirar Toyota Hiace da kuma babbar mota, wadda mutum uku da ke cikinta ba su ji ko ƙwazane ba.

A cewarsa, lamarin ya faru da misalin ƙarfe 4:40 na yamma, kuma jami’an hukumar sun isa wurin cikin minti bakwai da faruwarsa.

Ya ɗora alhakin hatsarin kan gudun wuce sa’a wanda ya haddasa motocin biyu suka yi karo da juna.

“Mutum 21 ne abin ya ritsa da su kuma akwai manya 18 da yara uku. !8 ɗin suna cikin bas ɗin kuma sun ƙone ƙurmus bayan ta kama da wuta sakamakon karon da ta yi da tirelar,” in ji shi.

nhgsfp

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp