Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta jihar Borno (SEMA) ta ce mutum 18 ne suka mutu a harin bom da wasu ‘yan ƙunan ɓakin wake suka tayar a wurin taron biki ranar Asabar a Gwoza da ke jihar.
Rahotonni sun ce fiye da mutum 30 ne suka samu munanan raunuka a harin, wanda ya kasance ɗaya daga cikin mafiya muni a baya-bayan nan.
Babban daraktan hukumar, Barkindo Saidu ne ya tabbatar da haka, yana mai cewa a kan idonsa bom na farko ya tashi.
Kamfanin dillancin labaran ƙasar, NAN ya ruwaito shi yana cewa “A gaban idona, da misalin ƙarfe 3:00 na rana, bom na farko ya tashi a Gwoza, wanda wata mace ta tayar bayan ta kutsa cikin taron bikin”.
Bayan tashin bom na farko, wanda ya jikkata fiye da mutum 30, tare da kashe wasu, sai na biyu ya sake tashi a kusa da babban asibitin yankin, in ji Barkindo Saidu.
”A yayin da mutane ke yi wa waɗanda suka mutu jana’iza, sai bom na uku ya tashi, inda nan ma wata mace ta tayar da shi tare da kashe wasu”, in ji daraktan na SEMA.
Ya ƙara da cewa bom na huɗu ya fashe ne a asibiti, wanda wata matashiya ta tayar a lokacin da jami’an hukumar da likitoci ke taimaka wa waɗanda hare-haren farko suka jikkata.
“Kawo yanzu mutum 18 ne suka suka mutu, da suka haɗa da maza da mata da ƙananan yara da mata masu juna biyu. Mutum 19 da suka samu munanan raunuka an kai su babban asibitin Maiduguri domin basu kulawar gaggawa” in ji Saidu.
Ya kuma ce akwai wasu ƙarin mutum 23 da ke jiran rakiyar sojoji domin kai su asibitin.
Tuni dai sojoji suka sanya dokar hana fita a faɗin ƙaramar hukumar Gwoza, sakamkon hare-haren.