Akalla ‘yan kasuwa 18 ne suka rasu a hatsarin mota kan hanyar su ta kai shanu zuwa Legas daga Sokoto a yammacin ranar Litinin.
A cewar rundunar ‘yan sandan jihar Kebbi, ta ce, an kai fasinjoji 42 da suka samu raunuka a hatsarin zuwa asibiti a yankin Gwandu da ke jihar.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, shanu 16 sun mutu a hatsarin.
Kakakin ‘yan sandan jihar, SP Nafiu Abubakar, ya ce hatsarin ya faru ne lokacin da direban wata babbar mota É—auke da fasinjoji da shanu daga yankin Illela na jihar Sokoto ya kauce hanya a mahaÉ—ar Malisa, inda nan take motar ta faÉ—i kasa.
Ya ce hakan ne ya janyo rasuwar fasinjoji 18 yayin da 42 kuma suka samu raunuka daban-daban.
SP Nafiu Abubakar ya kara da cewa kwamishinan ‘yan sandan jihar ta Kebbi, Ahmed Magaji Kontagora, ya tura jami’an ‘yan sanda zuwa wajen domin É—aukar waÉ—anda suka jikkata zuwa asibiti don yi musu magani.
Kwamishinan ‘yan sandan ya miÆ™a ta’azziya zuwa ga iyalan waÉ—anda suka rasu, inda kuma ya buÆ™aci kungiyoyin NURTW da NARTO da sauran masu amfani da hanya da su rika lura da abubuwan rage gudu da kaucewa É—aukar kaya fiye da Æ™ima da kuma mayar da hankali yayin tuki.