Mutanen da suka mutu sakamakon turmutsitsin da aka yi a wurin bikin Halloween a Koriya ta Kudu sun zama 153, kamar yadda hukumomi suka shaida wa BBC.
Jami’ai sun ce dubban mazauna birnin Seoul ne suka fita kan titunan domin yin bikin al’ada na shekara-shekara da aka saba yi, wanda shi ne irinsa na farko tun bayan É—age dokar sanya takunkumin yaki da cutar korona.
Wasu rahotannin sun bayyana yadda wasu ‘yan bikin suka dinga danne wasu saboda mummunan turmustsutsi har ta kai ga wasunsu na kwance kan wadanda aka danne.