Hukumar Kiyaye Aukuwar Haɗura FRSC, ta tabbatar da mutuwar mutum 15, da wasu mutum biyar kuma suka samu munanan raunuka a wani hatsarin mota da ya auku a jihar Kogi.
Kamfanin dillancin labaran (NAN), ya ruwaito cewa hatsarin ya auku ne bayan da wata motar fasinja ƙirar J-5 da wata tankar mai suka yi taho mu gama a garin Koton-Karfe da ke kan babbar hanyar Lokoja zuwa Abuja da safiyar ranar Talata.
Babban kwamandan Hukumar Kiyaye Aukuwar Hadura mai lura da jihar Stephen Dawulung, ya ce tuni aka kai wadanda suka samu raunukan asibiti domin ba su kulawar gaggawa.
Mista Dawulung ya ce saɓa dokokin hanya da direban motar fasinjan ya yi ne ya haddasa aukuwar hatsarin.