Hukumar kiyaye hadurra ta kasa (FRSC) a jihar Oyo, ta ce, mutane 146 ne suka mutu a wasu hadurran ababen hawa a jihar tsakanin watan Janairu zuwa Yuni.
Joshua Adekanye, Kwamandan hukumar na jihar ne ya bayyana hakan ga Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ranar Juma’a a Ibadan.
Ya kuma ce mutane 618 sun samu raunuka daban-daban a cikin hadurran mota 246 da aka samu a cikin wannan lokacin.
Da yake bayyana adadin, ya ce mutane 15 ne suka rasa rayukansu a watan Janairu; 15 a watan Fabrairu; 23 a watan Maris; Afrilu 24; 45 a watan Mayu da 24 a watan Yuni.


