Akalla mutum 14 ne suka rasu a wani hatsarin mota a ƙauyen Zangoro akan hanyar Bauchi-Darazo.
Lamarin ya faru afku ne jiya Alhamis. Babban kwamandan hukumar kiyaye haɗura reshen jihar ta Bauchi, Yusuf Abdullahi, shi ya bayyana faruwar hakan a wani rahoto kan yawan haɗura da ake samu a jihar, inda ya ce hatsarin ya kuma jikkata mutum biyar.
Ya ce hatsarin ya faru ne tsakanin wata mota kirar Golf da kuma Chevrolet.
Kwamandan ya danganta yawan haɗura da ake samu kan gudu fiye da ƙima da mutane ke yi, inda ya ce jami’ansa sun gano kuɗi N73,000 da wayoyin salula guda bakwai da kuma ƙananan jakukkuna a wurin da lamarin ya faru.
Abdullahi ya ce an ɗauki gawarwakin mutanen da suka rasu da kuma waɗanda suka jikkata zuwa Asibitin Koyarwa na Abubakar Tafawa Balewa.
Ya shawarci masu ababen hawa da su tabbata sun bi dokokin hanya domin ƙaucewa shiga hatsari.