Mutum 14 ne suka mutu sakamakon faduwar jrgin sama a yankin Amazon na Brazil. Karamin jirgin na kan hanyar zuwa Manaus na jihar Amazona, ya kuma fado sakamakon ruwan sama mai karfin gaske, daidai lokacin da ya fara ketara sararin Barcelos.
Dukkan fasinjoji 12 da ma’aikata 2 sun rasu, wanda yawanci ‘yan yawon bude ido ne da ke hanyar zuwa wasan kamun kifi.
Barcelos dai fitaccen yanki ne da ke daukar hankalin ‘yan yawon bude ido, wanda ke kusa da wurare masu Æ™ayatarwa da ban sha’awa.


