Rundunar ƴansandan jihar Edo ta sanar da kama mutum 14 da ake zargi suna da hannu a kashe matafiya a ranar Alhamis.
Matafiyan dai sun ratsa ta jihar ne a hanyarsu daga Fatakwal da ke kudancin Najeriya zuwa Kano da ke arewacin ƙasar, inda wasu ƴan sa-kai suka tare su a yankin Uromi bisa zargin masu garkuwa da mutane ne, wanda hakan ya sa mutanen yankin da suka musu aika-aikar.
A cewar kakakin rundunar ƴansandan jihar Edo, Moses Yamu, ya ce an kama wasu waɗanda ake zargi da hannu a kisan.
“A cigaba da bincike da muke yi, zuwa yanzu mun kama mutum 14 da ake zargi suna da hannu, sannan an yi taron gaggawa tsakanin dukkan masu ruwa da tsaki na yankin domin a kwantar da hankalin jama’a,” in ji Yamu a wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a.
Sai dai rundunar ta ƙara da cewa kawo ɗauki da ta yi ne ya taimaka wajen ceto mutum 10 daga cikin matafiyan.