Wasu matan aure da yara su kimanin 13 sun mutu a kasar India, sakamakon fadawa cikin wata rijiya, yayin bikin aure a Arewacin India.
‘Yan sanda sun tabbatar da faruwar lamarin a cikin kasar a sanar ranar Alhamis din nan.
Ta ce, wadanda abin ya ritsa da su lokacin suna zaune ne a kan wani murfin karfe da ya rufe rijiyar kwatsam sai ya rufta da su ciki.
Babban jami’in dan sanda, Akhil Kumar, ya shaidawa manema labarai a Kushinagar, Jihar Uttar Pradesh.