Rundunar ‘yan sandan jihar Filato ta tabbatar da cewa, mutane 13 ne suka rasa rayukansu yayin da wasu goma suka samu raunuka daban-daban, sakamakon fashewar tankar da ta tashi a karamar hukumar Jos ta Arewa.
Rundunar ta kuma ce shaguna 28, motoci takwas, babura uku shida da kuma babura biyu sun lalace a lamarin.
A ranar Larabar da ta gabata ne wata motar dakon mai dauke da Premium Motor Spirit (PMS) ta samu birki a kan hanyar Bauchi da ke karamar hukumar Jos ta Arewa inda ta fado inda ta yi tashin bam.
Rundunar ‘yan sandan ta bakin jami’in hulda da jama’a, Alfred Alabo, ta tabbatar wa manema labarai wannan adadi a Jos, babban birnin jihar a ranar Juma’a.
A cewarsa, “A ranar 27 ga Afrilu, 2023, da misalin karfe 13:30, wani mummunan hatsarin mota ya afku a mahadar titin Bauchi, inda wata motar tanka da ke dauke da man fetur ta bata birki, sannan ta kama wuta.
“Sakamakon kona shaguna ashirin da takwas, motoci takwas, babura uku guda shida da babura biyu.”
Ya ci gaba da bayanin cewa “An kona mutane 13 da ba a san ko su wanene ba, wanda hakan ya karu da abin da aka ruwaito a sakinmu da aka yi a baya.
“JNI ce ta binne gawarwakin kamar yadda addinin Musulunci ya tanada yayin da aka kai wadanda suka jikkata goma asibitoci daban-daban domin kula da lafiyarsu.
“Bayan haka kuma an bayyana cewa wasu fusatattun ’yan daruruwa sun kai hari kan ma’aikatan FRSC tare da kona motar aikinsu mai lamba AO1 783 RS, a yayin da daya daga cikin ma’aikatan FRSC ya samu raunuka a goshinsa.”
Alabo ya kuma ce an kama wani da ake zargi da hannu wajen kai harin.
Kakakin ‘yan sandan ya ci gaba da cewa, Kwamishinan ‘yan sandan Bartholomew Onyeka, ya tattara DOPS, DPOs na Area, da shugabannin Tactical Teams domin daukar matakan da suka dace domin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali da aka samu a yankin.