Hukumar kula da cututtuka masu yaɗuwa a Najeriya, NCDC ta tabbatar da ɓarkewar cutar zazzabin Dengue a jihar Sokoto.
Babban Daraktan hukumar ta NCDC, Dakta Ifedayo Adetifa wanda ya bayyana haka cikin wata sanarwa da aka fitar a Abuja, ya ce mutum 71 ake zargin sun kamu da cutar, an tabbatar da mutum 13 sun kamu sai dai babu rahoton asarar rai daga ƙananan hukumomin jihar uku da aka samu ɓullar cutar.
Adetifa ya bayyana cewa galibin mutanen da ake zargin sun kamu da cutar ƴan shekara tsakanin 21 da kuma 40 ne inda ya ce an gano hakan cikin watan Nuwambar 2023.
Babban daraktan hukumar ya ce ɓarkewar cutar a yanzu yana mataki na matsakaici la’akari da binciken da aka yi game da haɗarin cutar. Ya kuma ce akwai isassun kayan aiki da kuma ma’aikatan lafiyar da za su duƙufa ko da an samu ɓarkewar cutar a sauran jihohin ƙasar.
Adetifa ya shawarci ƴan Najeriya musamman mazauna jihar Sokoto da su yi riƙo da dukkan matakan kariya kamar sanya kayan da za su rufe jikinsu domin kare kansu daga cizon sauro sannan su kwanta a gidan sauro mai magani.
Sannan a cewarsa, ya kamata mutane su riƙa amfani da maganin sauro a wuraren da suke kwana tare da tabbatar da tsaftar muhallansu domin kare bai wa sauro mafaka.