fidelitybank

Mutane 12 sun mutu yayin wani hatsari a jihar Yobe

Date:

Mutane goma sha biyu sun mutu a wani haɗarin mota da ya faru a daren da ya gabata na Talata, a kan hanyar Bayamari zuwa Geidam a jihar Yobe da ke arewa maso gabashin Najeriya.

Mutanen sun ƙunshi maza manya goma da babbar mace ɗaya da kuma wata ‘yar ƙaramar yarinya ɗaya, kamar yadda shugaban hukumar kiyaye haɗura ta ƙasar, reshen jihar ta Yobe, Livinus Yilzoom ya bayyana a wata sanarwa ga manema labarai, a babban birnin jihar, Damaturu.

Kwamandan ya ce haɗarin ya faru ne da misalin ƙarfe goma na daren da ya gabata a ƙauyen Chelluri daidai kilomita 20, a kan hanyar Bayamari zuwa Geidam.

Ya ce haɗarin ya afku ne lokacin da motar da mutanen da suka rasu ke ciki, kirar Sharon ta yi karo da wata babbar mota ƙirar Howo ta wani kamfanin aikin gine-gine wadda take tsaye a hanya.

Mista Yilzoom, ya ce karon da Sharon ɗin ta yi ne ta kama da wuta kuma mutanen da ke cikinta suka ƙone yadda ba za a iya gane su ba.

vanguard news paper

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp