Yan sanda a arewa maso yammacin Uganda na bincike a kan mutuwar wasu mutum 12 da ake zargi sun sha wata barasa da aka yi a gida.
Rahotanni sun ce mutanen sun mutu ne a tsakanin ranakun Asabar da Lahadi a lardin Madi-Okollo.
Kazalika an kwantar da wasu da dama a asibiti bayan da suka sha barasar mai suna City 5 Pineapple Flavoured Gin, ciki har da mutumin da yake sayar da ita.
‘Yan sandan sun ce ba a kai ga gano abubuwan da ake hada barasar ba, to amma an bayyana cewa akwai ruwan da aka tace da karin wasu nau’ukan barasar a cikin abubuwan da aka yi amfani da su wajen hada barasar.
Mai magana da yawun rundunar a yankin da lamarin ya afku, ya ce, an karbi samfurin barasar domin gwaji da kuma bincike.
Sannan an kama wasu mutum hudu da ake zargi, kuma an rufe wajen da ake hada barasar.
Mutuwa bayan an sha barasa a Uganda ya zamo ruwan dare gama duniya, inda ko a 2010 sai da mutum 80 suka mutu a kudu maso yammacin kasar bayan sun sha barasa. In ji BBC.


