Hukumar Kiyaye Haddura ta Ƙasa (FRSC) reshen Kano, ta ce wani hatsari da ya faru da misalin ƙarfe 2:40 na Asuba a kan babban titin Zariya Mutane 12 sun mutu.
Kakakin FRSC a jihar, ya bayyana cewa lamarin ya shafi babbar motar tirela ta DAF CF95 wadda ke ɗauke da kaya da kuma fasinjoji.
“Mutum 12 daga cikin 19 da ke cikin motar sun mutu nan take, biyar sun jikkata, yayin da biyu suka tsira ba tare da wata matsala ba,” in ji FRSC.
An garzaya da waɗanda suka jikkata zuwa Asibitin Kura, yayin da aka ajiye gawarwakin mamatan a Asibitin Nassarawa.