Majalisar dokokin jihar Nasarawa ta ce, mutane 12 ne suka mutu a wani hatsarin kwale-kwale a kogin Kogi, Kungra Kamfani, a unguwar Arikiya da ke karamar hukumar Lafia a ranar 20 ga watan Agusta.
Alhaji Ibrahim Abdullahi, shugaban majalisar ne ya bayyana haka a wani taron gaggawa da majalisar ta gudanar a ranar Alhamis a garin Lafiya.
Abdullahi ya jajantawa kananan hukumomin jihar da na Lafia bisa afkuwar lamarin.
Ya kuma jajantawa iyalan wadanda suka rasu bisa rasuwar ‘yan uwansu.
“Abin bakin ciki ne matuka yadda muka rasa mutane 12 da suka hada da maza da mata a wani hatsarin jirgin ruwa a Arikiya da ke karamar hukumar Lafia.
“Mutane 19 ne ke cikin jirgin, 12 sun mutu sannan bakwai aka ceto. An jefa karamar hukumar Lafiya da jiharmu cikin alhini kan wannan lamari mai ban tausayi,” inji shi.
Majalisar wadda ta bayyana lamarin a matsayin abin takaici, sai dai ta bukaci ‘yan uwa da al’ummar karamar hukumar Lafia da gwamnatin jihar da su dauki wannan rashi da ba za a iya kwatantawa ba.
“A madadina, Honourable members da kuma ma’aikata, muna jajantawa iyalan mamatan, karamar hukumar Lafia da gwamnatin jihar bisa rasuwarsu.
“Muna addu’ar Allah ya hutar da rayukansu,” in ji kakakin.
Ya kuma yi addu’ar Allah ya gafarta wa wadanda abin ya shafa kurakuransu, ya kuma sa su huta.
Daga baya ‘yan majalisar sun yi shiru na minti daya domin girmama rayukan da suka rasu.


