Rundunar ‘yan sandan jihar Rivers ta tabbatar da cewa, mutane 12 ne suka mutu sakamakon fashewar wani abu da ya faru da safiyar Juma’a a kauyen Rumuekpe da ke karamar hukumar Emoha a jihar.
Kakakin rundunar ‘yan sandan, SP Grace Iringe-Koko, ta bayyana haka a cikin wata sanarwa da ta fitar a Fatakwal, inda ta ce binciken farko ya nuna cewa wadanda abin ya shafa na diban danyen man ne lokacin da wurin ya kama wuta.
Fashewar ta afku a daidai lokacin da wata motar bas dauke da danyen mai ta kama da wuta, a lokacin da take barin wurin zuwa wata matatar mai ta haramtacciyar hanya a yankin.
“Ya zuwa yanzu kimanin mutane 12 ana kyautata zaton sun kone kurmus. Har yanzu ba a san ko su waye wadanda abin ya shafa ba,” inji ta.
Iringe-Koko ya kuma ce an kona motoci biyar da babura uku hudu a wurin fashewar.
A halin da ake ciki, rundunar ‘yan sandan ta gargadi jama’a da su nisanta kansu daga hada-hadar man fetur ba bisa ka’ida ba, su tuntubi ta lambobin waya, 08032003514 da 08098880134, domin kai rahoton duk wani laifi.