Ƙungiyar agaji ta Red Cresent a Libya na cewa adadin mutanen da suka mutu sakamakon ambaliyar ruwa a yankin Derna sun kai dubu 11,000.
Sannan akwai yiwuwar alƙaluman su ƙaru yayin da ake cigaba da zaƙulo ƙarin gawarwaki a cikin laka.
Mahukunta na kiyasata cewa akwai mutane dubu 30 da suka rasa muhallansu yanzu haka.
Wakilin BBC ya ce “ba wai kawai yankin Derna ba ne ambaliyar ta shafa, kusan daukancin arewacin Libya masu manyan birane an tafka wannan barna.”
Ƴan siyasa a Libya sun nemi a gudanar da bincike domin gano yadda ambaliyar ta lalata madatsun ruwa biyu.
Akasarin ƴan kasar na zargin akwai sakaci na rashin kulawa.
Majalisar Ɗinkin Duniya ita ma ta soki yadda ƙasar ke tafiyar da tsare-tsarenta.


