fidelitybank

Mutane 11 sun kone kurmus a wani hadarin mota – FRSC

Date:

Mutum 11 sun ƙone ƙurmus a mummunan haɗarin mota da ya ritsa da ababe hawa daban-daban a yankin Ochadamu na Jihar Kogi.

Hukumar Kiyaye Haɗurra ta Ƙasa (FRSC), ta faɗa cikin wata sanarwa ranar Alhamis cewa hatsarin ya ritsa da ababen hawa 20.

Jami’in hulɗa da jama’a na FRSC, Bisi Kazeem, ya ce za a iya kare afkuwar haɗurran, yana mai kira ga masu ababen hawa da su dinga kula da abin hawan nasu akai-akai.

“Tawagar bincike ta ba da rahoton cewa lamarin ya ritsa da mutum 18,” in ji shi.

“Daga cikinsu, mutum bakwai – uku maza huɗu mata  sun ji raunuka daban-daban, yayin da sauran 11 ɗin waɗanda ba a iya tantance jinsinsu ba ya zuwa lokacin haɗa wannan rahoton suka ƙone ƙurmus.”

Ya ƙara da cewa rahoton ya bayyana dalilin faruwar hatsarin da lalacewar titi, da shanyewar birki, da rashin ingancin abin hawa.

breaking news in nigeria today

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp