Aƙalla mutum 10 sun mutu, ciki har da ƙananan yara, yayin da da dama suka samu raunuku sakamakon wani turmutsutsu da ya faru a cocin Catholic da ke unguwar Maitama a Abuja.
Lamarin ya faru ne ya faru ne ranar Asabar da safe lokacin da mutane suka yi dafifi a harabar cocin domin karɓar kayan tallafi da ta alƙawarta raba wa marasa ƙarfi da tsofaffi.
Cikin wata sanarwa da rundunar ‘yansandan birnin Abuja ta fitar, ta ce cikin waɗanda suka mutu har da ƙananan yara huɗu, yayin da mutum takwas suka samu munanan raunuka, kuma suke karɓar magani a asibiti.
‘Yansandan sun ce jami’an tsaro sun samu nasarar korar duka mutanen da suka taru a cocin waɗanda ta ce sun kai fiye da mutum 1,000.