Wani sashe na al’ummar Musulmai a Kenya sun zargi gwamnatin ƙasar da kawo ruɗani a ganin wata bayan ta ayyana Juma’a a matsayin ranar hutun sallah.
Ministan harkokin cikin gida Kithure Kindiki ne ya ayyana hutun a ranar Laraba a wata sanarwar da gwamnati ta fitar.
Shugaban Majalisar Koli ta Musulmi a Kenya, Hassan Ole Naado, ya shaida wa shafin intanet na Nation cewa sanarwar da gwamnatin ƙasar ta yi ya ruɗa al’ummar musulmi domin bai kamata ba har sai an ga watan sallah.
Mista Naado ya ce, ba gwamnati ce ke da hurumin sanar da kawo karshen watan Ramadan ba, inda ya ce shugaban majalisar koli ta Musulmi shi ke da ikon yin hakan.
“Ya kamata gwamnati ta tuntuɓi Musulmi kafin ta yanke hukunci. Wannan babban kuskure ne kuma mai ruɗarwa,” inji shi.
Musulmai da dama a ƙasar sun yi Alla-wadai da matakin gwamnatin a shafukan sada zumunta


