fidelitybank

Musulmai a Habasha sun gamu da cikas yayin Sallar Idi

Date:

Jami’an tsaro a Addis Ababa, babban birnin Ethiopia, sun fesa barkokon-tsohuwa kan wasu Musulmai da suka taru domin gudanar da sallar Idi.

Dubban Musulmai ne suka taru a babban filin wasan birnin inda kuma a nan ake sallar Idi amma rikici ya barke. Ba a samu rahoton mutuwa ba.

Lamarin ya faru ne kwanaki kadan bayan da aka tayar da jijiyoyin wuya tsakanin Musulmai da Kiristoci a sassan kasar bayan an kashe Musulmai 20 da ke halartar jana’iza a makon jiya a arewacin Ethiopia.

Bayan aukuwar lamarin a birnin Gondar, an gudanar da jerin zanga-zanga a wurare da dama da kuma tarzoma ciki har da kona akalla coci uku a kudancin kasar.

Matakin da jami’an tsaro suka dauka na fesa barkonon-tsohuwa kan Musulman zai iya dagula lamura.

An ga hotunan mutane suna tserewa yayin da ake wurga musu barkonon-tsohuwa da kuma mata da ke neman ‘ya’yansu cikin kaduwa.

Rundunar ‘yan sandan Addis Ababa ta dora alhakin lamarin kan “wasu tsirarun mutane” kuma ta ce an lalata wurare da dama. A cewar BBC.

legitnews.com

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp