fidelitybank

Murja ‘yar TikTok na amsa tambayoyi daga EFCC

Date:

Hukumar EFCC ta sanar da kama fitacciyar ƴar TikTok, Murja Ibrahim Kunya saboda zargin laifin wulaƙanta takardun kuɗin Najeriya, wato naira.

Ofishin shiyya na hukumar da ke Kano ne ya sanar da hakan a cikin wata sanarwar da suka fitar, inda hukumar ta ce an kama ta ne bisa zarginta da wulaƙanta kuɗin Najeriya.

“An kama Murja Kunya ne bisa zarginta da wulakanta takardun kuɗin naira a lokacin da take zaune a otel ɗin Tahir Guest Palace a Kano. An sake kama ta ne bayan da farko ta tsere daga belin da hukumar ta ba ta kimanin wata ɗaya da ya gabata.

“Da farko an kama ta ne a watan Janairun 2025 bayan saɓa dokar amfani da kuɗi na babban bankin Najeriya, wadda ta hana wulaƙanta takardun kuɗin Najeriya wato naira. Sai hukumar ta bayar da belinta kafin a gabatar da ita a kotu a Kano, da lokacin zuwa kotu ya yi sai ta tsere, aka neme ta aka rasa.”

“Bayan makonni ana nemanta ne jami’anmu suka kama ta a ranar Lahadi 16 ga watan Maris, sannan aka mayar da ita ofishin hukumar da ke Kano.”

Sanarwar ta ƙara da cewa hukumar na shirye-shiryen gabatar da ita a kotu.

legit breaking news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp