Shugaban kasar Faransa, Emmanuel Macron, ya yi kakkausar suka kan matsayin da shugabannin kasashen Afirka suka dauka a kan yakin Ukraine.
Mista Macron ya yi tir da abinda ya kira ”Munafurcin kasashen Afirka”’ wadanda suka ki yarda cewa Rasha na yaki a Ukraine.
Shugaban na Faransa na wannan jawabi ne a birnin Yaoundé na kasar kamaru a wata ziyara da yake yi a kasashen Afirka
Wasu daga cikin kasashen nahiyar Afirka sun ki fitowa fili su soki Rasha, saboda yakin da take a Ukraine.
A watan Maris kasashen Afirka da dama sun ki halartar taron da Majalisar Dinkin Duniya ta kira domin yin Allah wadai da mamayar da Rasha ke yi a Ukraine;
Mujallar Journal du Cameroun ta ruwaito cewa, shugabannin biyu za su tattauna batun mayakan jihadi irinsu Boko hakaram da ke yi wa arewacin Kamaro barazana, da kuma batun ‘yan awaren Ambazoniya.
Shugaban na Faransa na ziyarar kasashen Afirka uku, inda ake sa ran zai tattauna batun karancin abinci, da rikice-rikice tare kuma da batun alaka tsakanin Faransa da kasashen nahiyar. In ji BBC.