fidelitybank

Muna ƙara jaddada cewa ba mu da hannu a zanga-zangar Najeriya – Rasha

Date:

Gwamnatin Rasha ta nesanta kanta da wasu masu zanga-zanga a Najeriya waɗanda aka gani suna ɗaga tutar ƙasar Rasha.

A ranar Litinin an ga tuɗaɗowar ɗumbin masu zanga -zanga a jihohin arewacin Najeriya kamar Zamfara da Kaduna tare da jihar Kano, inda wasu daga cikinsu ke ɗaga tutar Rasha.

Sai dai a wata sanarwa da aka sanya a shafin na intanet, ofishin jakadancin Rasha a Najeriya ya ce, matakin da wasu masu zanga-zanga suka ɗauka na amfani da tutar Rasha mataki ne na ƙashin kansu, kuma wannan ba shi ne ainahin manufa da muradin ƙasar Rasha ba.

Sanarwar ta ce: “Kamar a kodayaushe, muna sake jaddada cewa Rasha ba ta shiga cikin harkokin cikin gida na ƙasashe masu ƴanci, ciki kuwa har da Najeriya.”

Rasha ta ce tana martaba mulkin dimokuraɗiyyar Najeriya, kuma tana kyautata zaton cewa zanga-zangar da ake yi a ƙasar na kan doka da kuma tsari na mulkin demokuraɗiyya.

Sanarwar ta kammala da cewa “sai dai za mu yi Allah-wadai idan wannan zanga-zanga ta rikiɗe zuwa tarzoma.”

Dubban masu zanga-zanga ne suka hau kan titunan biranen Najeriya a zanga-zangar adawa da matsin rayuwa da al’ummar ƙasar ke ciki.

Zanga-zangar ta ci gaba a ranar Litinin bayan da ƙungiyoyin da ke jagorantarta suka ce jawabin da shugaban ƙasa ya yi a ranar Lahadi bai taɓo buƙatunsu ba.

An tsara gudanar da zanga-zangar ne tsawon kwana goma, daga 1 zuwa 10 ga watan Agustan 2024.

nigeria news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Kare Ya Kashe Ragon Layya: Mai ƙwacen waya ya kashe Sojin ruwa a Kaduna

Wani mai ƙwacen waya ya kashe wani soja bayan...

Sojoji sun hallaka ƴan Boko Haram da dama

Da sanyin safiyar ranar Litinin, dakarun rundunar Haɗin kai...

Tarzomar kama baƙin haure a Amurka na yamutsa hazo

An shiga rana ta uku a tarzomar da ake...

Alhazai sun kammala aikin Hajji bana

A ranar Lahadin da ta gabata ne alhazai miliyan...

Tinubu gyaran ƙasa za ka mayar da kai ba zaɓen 2027 ba – ACF

Ƙungiyar Tuntuɓar Juna ta Arewacin Najeriya, ta yi kira...

Ƴan Jagaliya sun caka wa Matashi kuwa lokacin da ya zo karɓar naman Sallah a Kano

Matashi Ibrahim Mahmud ya rasu sakamakon caka masa wuƙa...

Kallo Ya Koma Sama: Elon Musk zai fuskanci mummunar sakamako – Trump

Ana ci gaba da takun saka tsakanin shugaban Amurka...

Zulum ya miƙa kyautar Naira miliyan 100 ga iyalan Sojojin da aka kashe

Gwamna Babagana Umara Zulum na jihar Borno, ya bai...

Otal ɗin ƴan Najeriya ya kama da wuta wani ɓangaren a Saudiyya

Hukumar Alhazai ta Najeriya ta ce an samu tashin...

An kai hari maɓoyar Boko Haram a Borno

Biyo bayan sahihan bayanan sirri da aka samu, rundunar...

Alaƙar Trump da Elon Musk ta yi tsami sosai

Attajirin da ya fi kowa arziki a duniya, Elon...

An yi jana’izar Muhammad Uwais

An gudanar da jana'izar tsohon alkalin alkalan Najeriya, mai...
X whatsapp