Jagoran addini na Iran Ayatollah Ali Khamenei ya musanta hannun ƙasarsa a munanan hare-haren da kungiyar Hamas ta ƙaddamar kan Isra’ila ranar Asabar.
Amma a cewar fassarar da kamfanin dillancin labarai na Reuters, Khamenei ya ce: “Muna yaba wa waɗanda suka shirya kai hari a kan gwamnatin masu tsananin kishin Yahudanci”.
A matsayin tunatarwa, an san Iran tana ba da kuɗade ga Hamas, da kuma ba da horo da makamai ga mayakan Hamas