fidelitybank

Muna tunanin cire tallafin mai ba tare da ya shafi ƴan Najeriya ba – Gwamnati

Date:

Gwamnatin tarayya ta ce, tana nazari a kan hanya mafi dacewa ta cire tallafin man fetur, ba tare da an kawo cikas ga harkokin rayuwa a ƙasar ba.

Babban sakatare a ma’aikatar albarkatun man fetur, Ambasada Gabriel Aduda ne ya bayyana haka lokacin da yake jawabi ga manema labarai a ƙarshen Taron Ƙoli kan Makamashi na Duniya a Najeriya.

Ya ce gwamnati tabbas ta duƙufa kan aniyar cire tallafin man fetur, amma ba ta sa ranar yin hakan ba, don kuwa sai ta gama nazarin duk alƙaluma da nufin ganin raɗaɗin da lamarin zai kawo, bai kasance mai tsanani ga masu ƙaramin ƙarfi a Najeriya ba.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN ya ruwaito Aduda na cewa ko da yake cire tallafin man fetur abu ne da aka mayar da hankali kansa tsawon lokaci, amma Shugaba Buhari kuma ministan albarkatun mai yana ɗaukar lamarin da gaske, kuma yana tuntuɓar kowa da kowa a ɓangaren samar da mai.

A cewarsa har yanzu, jami’an gwamnati na duban tsanaki kan yadda za a cire tallafin ba tare da al’amuran raryuwa sun hargitse ba.

Ya ce nauyi ne a kansu a matsayinsu na gwamnati, don haka tabbas sai sun kawo matakan da za su rage raɗaɗi kuma a samar da canjin ƙasashen waje ta yadda ‘yan kasuwa za su iya samu cikin sauƙi don shigo da kayan da ake buƙata.

Gabriel Aduda ya tabbatar da cewa sai sun samar da kuɗaɗen canjin waje na aƙalla wata shida ta yadda ko an samu akasi, rayuwa ba ta tagayyara ba

breaking news in nigeria today punch

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp